‘Yan sandan Turai sun kame gwamman masu damfarar mutane ta Intanet

Jami’an tsaro sun chafke akalla mutane 150 da ake zargi da hannu wajen aikata laifukan damfarar mutane ta intenet, a fadin duniya, a cewar rundunar ‘yan sandan tarayyar Turai.

Ana zargin mutanen da aka kama da hannu wajen kirkirar haramtattun shafukan Intenet domin damfarar mutanen ta hanyar sayar musu da kayayyaki marasa inganci, ko kuma kulla kasuwanci na bogi da sauran laifuka.

Sashen ‘yan sandan turai na Operation DarkHunTOR ne ya kaddamar da aikin kama mutanen, wanda kuma aka kwato miliyoyin euro na tsabar kudi da kuma kudaden Intenet na Bitcoin da bindigogi da kuma muggan kwayoyi.

‘Yan sandan sun ce alamu na nuni da cewa aikata badakala ta kan interenet na sake samun gurin zama a zukatan jama’a musamman matasa ta yadda suke samar da kasuwanni na bogi don karbewa mutane kudade da kadarorinsu.

An dai kama mutanen ne a kasashen Australia, Bulgaria, France, Germany, Italy, Netherlands, Switzerland, Burtaniya da kuma Amurka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *