Pogba ya sauke batun tsawaita kwantiraginsa a United saboda Solskjaer

Dan wasan Manchester United, Paul Pogba ya jingine batun sabatanta kwantiraginsa a Old Traford, bayan da yayi watsi da kocinsa Ole Gunner Solskjaer, bayan da aka bashi jan kati a lokacin da yeke fitcewa daga fili a karawar da Liverpool ta doke su da 5-0 ranar Lahadi. (Sun)

Manchester United ta rubuta jerin sunayen mutane huɗu da take sa ran ɗaya daga cikinsu zai maye gurbin Solskjaer wanda ke fuskanatar matsin lamba a halin yanzu, wadanda suka haɗa da Zinedine Zidane da Antonio Conte da kocin Leicester Brendan Rodgers da kocin Ajax Erik ten Hag. (Sun)

Yayin da jaridar Telegraph tace an baiwa Solskjaer wasanni uku kachal don ceto aikinsa a kungiyar. (Telegraph – ana buƙatar biyan kuɗi)

Amma har yanzu ana ganin kocin Paris St-Germain Mauricio Pochettino mai shekara 49  a matsayin na sahun gaba na Manchester wajen maye gurbin Solskjaer. (Star)

Barcelona na sa ran ɗauko kocin Liverpool ɗan ƙasar Jamus Jurgen Klopp mai shekara 54 domin maye gurbin Ronald Koeman. (Sport – in Spanish)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *