Harin ta’addanci ya kashe sojojin Burkina Faso uku

Sojojin Burkina Faso uku  sun gamu da ajalinsu, wasu bakwai kuma suka jikkata,  a wani kazamin hari da aka kai masu a daidai kan iyaka da kasar Ivory Coast.

Tuni dai wasu majiyoyin samun labarai na kasar suka gaskata wannan hari.

Tun shekara ta 2015 ne dai kasar Burkina Faso ke fuskantar yawaitan hare-hare daga masu ikirarin jihadi da karfin tsiya da suka mamaye yankunan kasashen Mali, Nijar.

Majiyoyin samun labarai sun bayyana cewa babu wanda zai iya gane wadannan mahara, da suka kai harin a yankin Mangodara a daidai karfe 9  na daren littini.

Raunin da wasu suka samu yayin wannan hari babu kyau.

Sai dai kuma wasu majiyoyin na cewa sojan sun sami nasarar kasha masu jihadin 6.

Mako daya kenan aka sami irin wannan hari, inda aka jikkata wani dan-sanda, da kasha wani mahari a kauyen Tehini dake kan iyakan Burkina da Ivory Coast

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *