Chelsea da Arsenal sun haye zuwa Quater finals a gasar Carabao

Chelsea ta tsallake zuwa matakin daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin Carabao bayan ta doke abokiyar hamayyarta Southampton a bugun fanariti bayan sun tashi wasa 1-1.

Karo na biyu a jere kenan Chelsea ke bukatar bugun daga kai sai mai tsaron gida don kaiwa matakin wasan Quater Finals a gasar cin kofin Carabao, yayin da Arsenal da ta samu canji sosai ta doke Leeds da ci 2-0 a ranar Talata.

Kepa Arrizabalaga shi ne ya kasance gwarzon Chelsea, bayan da ya zura kwallon da ya bada tazarar bugun daga kai sai mai tsaron gida inda ya hana Saints gurbi a wasan da suka fafata a Stamford Bridge da ci 4-3, bayan kammala mintuna 90 a kunnen doki 1-1.

Arsenal

To, Chambers ya taimakawa Gunners kaiwa wasan kusa dana karshe na cin kofin Carabao.

Calum Chambers ya shigo wasan bayan hutun rabin lokaci, kuma ya taimaka wa Arsenal wajen samun nasara a kan Leeds da ci 2-0 a zagaye na hudu na gasar cin kofin Carabao.

‘Yan dakika kadan bayan maye gurbin Ben White da ya ji rauni mintuna 10 bayan dawowa daga hutu, Chambers ya zura kwallon farko duk da kokarin da mai tsaron gidan Leeds Illan Meslier ya yi.

Eddie Nketiah ne ya zura kwallo na biyu da ya baiwa Arsenal nasara kan Leeds ta ci 2 – 0.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *