Taron saka jari da ake gudanarwa a Saudiyya dama ce ta gabatar da buƙatu da cin gajiyar taron.
Taron na kwana uku wanda aka soma a ranar Talata shi ne karo na biyar da Sarkin Saudiyya ke jagoranta a Riyadh babban birnin ƙasar.
Taron ya ƙunshi shugabannin ƙasashe da manyan ƴan kasuwa masu saka jari da bankuna, kuma an bayyana cewa ya ƙunshi kamfanoni sama da 5,000 da ke halartar taron.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana cikin shugabannin duniya da suka halarci taron wanda aka yi wa take da ‘zuba jari kan inganta rayuwar al’umma’.
A cikin jawabin da ya gabatar a wurin taron, shugaba Buhari ya ce Najeriya ta mayar da hankali kan wasu manufofi na ci gaba, ta hanyar rage dogaro da arzikin fetir zuwa noma da fasahar sadarwa da kuma ma’adinai.
Ƙasar kuma a cewar Buhari ta mayar da hankali kan yaƙi da rashawa da matsalar tsaro da sauyin yanayi da ƙaddamar da shirin tallafawa al’umma.
Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu a hirarsa da BBC game da taron ya ce “taro ne da za a iya kiransa kamar tsarin bajekoli” tare da bayyana wasu guzurin buƙatu da Najeriya ta gabatar a taron.