Bankin Duniya ya dakatar da tallafin da yake baiwa Sudan

Bankin Duniya ya sanar da dakatar da tallafin da yake bai wa Sudan biyo bayan mamayar da sojoji suka yi da suka hambarar da firaministan kasar.

“Na damu matuka game da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a Sudan, kuma ina fargabar irin gagarumin tasirin da hakan zai iya yi ga farfadowar zamantakewa da tattalin arzikin kasar,” in ji shugaban bankin duniya David Malpass a cikin wata sanarwa.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da Sojoji a Sudan suka dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin sama na Khartoum har sai nan da ranar 30 ga watan da muke ciki na Oktoba, ko kuma idan an ga yanayin tsaro a kasar, biyo bayan juyin mulki.

Janar Ibrahim Adlan wanda shine ke rike da ikon kula zirga-zirgar jiragen saman kasar ya ce daga yanzu an dakatar da sauka  da tashin jiragen sama a filin jirgin saman Khartoum, har sai ranar 30 ga watan Octoban da muke ciki.

Wannan na zuwa ne bayan da Sojojin ke ci gaba da Fuskantar matsin lamba daga hukumomin duniya har ma da majalisar dinkin duniya kan bukatar su saki Franminista minista Abdallah Hamdok da suke tsare da shi.

Majalisar dinkin duniya na wannan kira ne bayan da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniyar ya gudanar da taron gaggawa kan halin da ake ciki a Sudan din bayan juyin Mulki da kuma tashin hankalin da ya biyo baya.

A jawabin da sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya gabatar, ya bukaci sojojin da su gaggauta sakin Abdallah Hamdok da ministocin da suka yi aiki karkashin gwamnatin hadakar.

Tuni dai Abdelfatah Al-Burhan ya mayarwa majalisar dinkin duniyar Martani inda ya ce Abdallah Hamdok na tsare ne a gidan sa kuma yana cikin yanayi mai kyau, kuma an tsare shine don kare lafiya, kuma da zarar abubuwan sun lafa to zai koma gurin iyalin sa cikin aminci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *