‘Yan bindiga sun kashe masu ibada yayin sallar asuba Neja

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja a Najeriya ta ce ‘yan bindiga sun kashe masu ibada 18 ba a yayin da suke sallar asuba a wani masallaci a kauyen Mazakuka dake karamar hukumar Mashegu ta jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Kuryas ne ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Najeriya wannan aika aika da ‘yan bindiga suka aikata a yayin wata ganawa a Minna, inda ya ce maharan sun yi awon gaba da mutane 17.

Mr Kuryas ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 da rabi na asubahin Litinin ta ranar 25 ga watan Oktoba, a lokacin da ‘yan bindigan suka kai hari kauyen.

Ya ce daga bisani ‘yan bindigan sun barnata kadarar da kudinsa ya tasam ma miliyoyin Nairori, mallakin wani Abubakar Maigandus a kauyen.

Ya karkare da cewa jami’an tsaro sun bindige daya daga cikin maharani har lahira.

Leave a Reply

Your email address will not be published.