Solskjaer ya tsallake rijiya da baya kan makomar aikinsa a United

Rahotanni daga Ingila na cewa mai yiwuwa kocin Manchster United Ole Gunnar Solskjaer ya tsallake rijiya da baya, sakamakon jinkirta korarsa daga bakin aiki da shugabannin kungiyar suka yi.

Sai dai fitacciyar kafar watsa labaran wasanni ta ESPN dake Amurka ta ruwaito cewa bayan taron da suka gudanar, shugabannun na United sun fito fili sun shaidawa Solksjaer cewar makomar aikin horaswar nasa na cikin halin rashin tabbas.

Zalika sun bashi wa’adin wasanni uku don ceton aikinsa, abinda ke nufin tsohon dan wasan na Red Devils ne zai jagoranci karawar da kungiyar za ta yi da Tottenham a gasar frimiyar Ingila a ranar Asabar mai zuwa.

Kocin na Man United ya zama abin muhawara a baya bayan nan bayan da Liverpool ta yi tattaki ta lallasasu har gida a filin wasa na Old Trafford da kwallaye 5-0 a ranar Lahadin da ta gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published.