Masu zanga-zangar Sudan sun yi tsayuwar gwamen Jaki kan aniyarsu

Al’ummar Sudan sun kwarara kan tituna cikin zanga-zangar nuna adawa da juyin mulki da sojoji suka sake yi a ranar Litinin, abinda ya kawo karshen gwamnatin hadakar kasar karkashin jagorancin Firaminista Abdallah Hamdok.

Tuni dai manyan kasashe da kungiyoyin duniya suka yi tir da wannan juyin mulkin da suka ce cikas ne ga ci gaban dimokradiyya da kuma koma baya ga kasashen Afirka.

Ana sa ran kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai yi wani taron gaggawa kan batun.

Tuni dai wasu jakadun kasashen Turai 3 suka fice daga Sudan, domin nuna fushin kasashen duniya game da juyin mulkin da aka yi a kasar, da kuma ayyana ofisoshinsu a matsayin na mutanen Sudan.

Masu zanga-zangar adawa da sake juyin mulkin da sojoji suka yi a Sudan. AFP – –

Jakadun kasashen da suka bar Sudan din sun hada da na Faransa, Belgium da Switzerland, wadanda suka ce, suna tare da jama’ar Sudan dari bisa dari, kuma basa goyon bayan juyin mulki ta kowacce fuska.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *