Mahukuntan jihar Naija a Najeriya sun bayyana daukar wasu matakan gaggawa sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai wani Masallaci a kauyen Maza-kuka da ke karamar hukumar Mashegu, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 18, wasu kuma da dama suka jikkata, sannan kuma maharan suka yi awon gaba da wasu mutanen 18.