Katafaren kamfanin hada-hadar cinikayya ta koma da ruwanka a duniya dake Amurka wato Sotheby, ya bayyana sayar da wasu takalma da fitaccen dan wasan kwallon Kwando na duniya Micheal Jordan yayi amfani dasu, a kan kusan dala miliyan 1.5 a ranar Lahadin da ta gabata.
Takalman na Mikel Jordan da kamfanin na Sotheby ya yi gwanjonsu farare ne masu ratsin ja da kamfanin Nike ya sana’anta Nike.Gwarzon dan wasan kwallon kwandon yayi amfani da su ne tun daga shekararsa ta farko a tare da kungiyarsa ta Chicago Bulls daga shekarar 1984 zuwa 1989.
Takalman wasannin na Michael Jordan sun zama mafi tsada da aka yi gwanjonsu ne bayan sayar dasu kan dalar Amurka miliyan 1 da dubu 472,000 a birnin Las Vegas.