Shugaban Turkiya ya bada umarnin korar Jakadun kasashe 10

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya baiwa ministan harkokin wajensa umarnin korar jakadun kasashe 10, cikinsu har da na Jamus da Amurka wadanda suka nemi sakin wani shugaban kungiyoyin farar hula da aka daure bisa zarginsa da cin amanar kasa.

Tuni dai shugaban na Turkiya ya janyewa jakadun kasashen 10 dukkanin matakan kariyar diflomasiya a yau Asabar, matakin farko da ake dauka kafin korar da ake shirin yi musu, wand aba a tsaida wa rana ba.

Wannan mataki dai ya biyo bayan sanarwar hadin gwiwar da Jakadun suka fitar a ranar Litinin da ta gabata, inda suka ce ci gaba da tsare Osman Kavala dan gwagwarmayar na yi wa Turkiyya barazana.

Jakadun kasashen da suka fitar da wannan sanarwa sun hada da na Amurka, Jamus, Canada, Denmark, da Finland. Sai kuma na Faransa, Netherlands, New Zealand, Norway da Sweden.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *