Shugaba Buhari zai halarci taron zuba jari a birnin Riyadh

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari zai bar kasar yau Littini zuwa kasar Saudiya inda ake taron Shugabannin kasashen Duniya game da  zuba hannun jari  karo na 5 da za’a yi a birnin Riyadh.

Shugaban na Najeriya zai yi wannan tafiya a wani lokaci da hukumomin kasar karkashin shugabancin sa ke ruwa da tsaki wajen farfado da tattalin arzikin. ta ga baki daya.

Taron na Riyadh zai taimakawa kasashen Duniya wajen tattance hanyoyin magance tarin tsaiko da tattalin arzikin su ke fuskanta a wannan lokaci da cutar Covid -19 ke haifar da tsaiko a fanonin da suka shafi zamantakewa da kasuwanci.

Kudaden kasashen Duniya
Kudaden kasashen Duniya REUTERS – STRINGER

Majiya daga fadar Shugaban ta Najeriya  na nuni cewa Shugaba Buhari tareda rakiyyar mukaranban sa za su yi amfani da wannan dama don gudanar da ayukan Umara a wannan lokaci da Saudiya ta kawo karshen bada tazara a fadin. kasar musaman a masallatai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *