Jamian tsaron Najeriya na farautar fursunonin da suka tsere a jihar Oyo

Ministan harakokin cikin gidan Najeriya Rauf Aregbesola ya bada tabbacin suna kokarin kamu fursunoni  392 da aka rasa inda suka tafi bayan tarzomar da ta barke a gidan yarin garin Oyo a jihar Oyo daren Juma’a. Ministan na bada wannan tabbaci ne yayin wata ziyara da ya kai garin na Oyo.

Kakakin hukumar Kula da gidajen kaso na kasar  Olarenwaju Anjorin ya fadi cikin wata sanarwa cewa fursunonin  837 suka tsere da fari, bayan da suka fasa garun ginin gidan yarin da nakiyoyi.

Bayanai nan una fursunoni 262 suka koma gidan kason amman kuma 575 babu wanda ya san inda suka yi.

A cewar Hukumomin kula da gidajen yarin, jamian tsaro dake kula da gidan yarin sun yi ta maza sun fafata da sojan hayan da suka kaiwa gidan kason hari.

Leave a Reply

Your email address will not be published.