Isra’ila za ta gina matsugunan Yahudawa sama da 1,300 a yankin Falasdinu

Isra’ila ta bayyana shirinta na gina karin gidaje sama da dubu daya da dari 3 don tsugunar da Yahudawa ‘yan kama wuri zauna a yankin yamma da tekun Jordanda ta mamaye.

Sanarwar da ta fito daga ma’aikatar samar da  gidaje  ta gwamnatin Fira minista Naftali Bennett ta ce an bada ayyukan gina gidaje guda dubu 1 da dari 3 da 55 a yamma da kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye tun a shekarar 1967 da aka yi yakin kwanaki 6.

Wadannan sabbin gidaje, kari ne a kan sama da gidaje 2000, wadanda majiyoyin tsaro suka ce za a ba mazauna cikinsu  takardun izinin zama a yankin, lamarin da  ya janyo caccaka daga Falasdinawa, masu fafutukar lalubo zaman lafiya da kuma makwafciyarta, Jordan.

A wata sanarwa, ministan samar da gidajen Isra’ila Zeev Elkin, wanda dan jam’iyyar New Hope party mai ra’ayin mazan jiya ne, ya ce jaddada kasancewar Yahudawa a yamma da kogin Jordan yana da mahimmancin ga manufofin akidar Zionism.

Da yake jawabi a taron mako mako na majalisar zartaswar Falasdinawa, Firaminista Mohammed Shtayyeh ya yi kira ga majalisar dinkin duniya da musamman ma Amurka da su tinkari Isra’ila a kan wannan mataki da take daf da dauka.

Kimanin Yahudawa dubu 475,000 ne suka share wuri suka zauna a Yamma da kogin Jordan, inda Falasdinawa ke kallo a matsayin makomarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.