ICC ta nemi gudanar da bincike a kan satar dalibai a arewacin Najeriya

Babban mai gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ya shirya don neman izinin gudanar da bincike a kan batutuwan da suka shafi satar dalibai a yankuna da dama na arewacin Najeriya.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwar da hukumar  kare hakkin dan adam ta SERAP ta fitar a yau Lahadi.

Abubuwan da za  a gudanar da bincike a kansu sun hada da rufe makarantu da kuma gazawar hukmomin Najeriya a matakin gwamnatin tarayya da na jihohi wajen kawo karshen garkuwa da dalibai.

A cewar daraktan hukumar, Kolawale Oluwadare, matakin kotun hukunta manyan laifukan ya biyo bayan wasikar korafi ne da hukumar ta aike mata, inda ta bukaci mai gabatar da kara, Karim Khan da ya tabbatar da hukunta wadanda ake zargin su na da hannu a aika aikar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *