Fararen hula da jami’an tsaro 944 yan bindiga suka kashe a Najeriya a watan Satumba

A Nigeria, Wani sabon rahoto daga wata kungiya mai suna West Africa Network for Peace Building dake sa idanu kan kisan da ‘yan bindiga ke yi na cewa a watan jiya kawai, rayukan mutane kusa fararen hula  da jamian tsaro 944 ‘yan bindiga suka kashe a hare-hare daban-daban a cikin kasar.TALLA

Rahoton daga wannan kungiya na nuni ta yada hare-haren suka fi muni a wasu yankunan kasar,sai dai duk da kokarin hukumomi na kawo karshen wannan matsala ,jama’a na ci gaba da kokawa a kai.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
‘Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost

Baya ga matsalar Boko Haram,yan bidinga da masu garkuwa da jama’a sun kawo durkushewar harakokin kasuwanci da noma a kauyuka da dama a Najeriya,wanda hakan ke tilastawa mutanen karkara tserewa daga yankunan su.

A cewar rahoton an yi kisan ne a dukkan sassan kasar ta Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *