Nijar ta cafke mutanen da ake zargi da kashe ma’aikatan agajin Faransa

Hukumomin Jamhuriuyar Nijar sun sanar da kama mutane 11 da ake zargin suna da hannu a kisan gillar da aka yi wa wasu ma’aikatan agaji guda 6 ‘yan kasar Faransa tare da dan rakiya da kuma direban su ‘yan Nijar a watan Agustan shekarar bara.

Bayanan dake zuwa daga Nijar sun ce a cikin watannin da suka gabata aka kama mutanen 11 da ake zargi da kashe ma’aikatan agajin na Faransa guda 6 da ‘yan Nijar guda biyu da suka hada da dan rakiyar su da kuma direban su.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce daga cikin wadanda aka kama har da mutum guda dake kula da su da kuma wani mai shiga tsakani.

Sauran sun fito ne daga wata kungiyar da aka rusa a Yamai da kuma kauyen dake kusa Koure mai gandun daji, inda ‘yan bindiga 3 akan babura suka yi farautar motar su da makamai.

Majiyar dake da labarin abinda ya faru, ta tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na AFP kama mutanen 11, amma kuma ba’a iya kama maharan guda 3 ba, duk da yake an gano ku su waye.

Rahotanni sun ce an kama mutanen 11 tsakanin watan Agustan bara zuwa Fabarairun bana, kuma tuni aka gabatar da su a gaban alkali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *