Fashewar bututun mai yayi sanadin kashe mutane da dama a Rivers

Rahotanni daga Najeriya sun nuna cewar akalla mutane 20 ake fargabar sun mutu a Jihar Rivers sakamakon fashewar bututun man fetur a karamar hukumar Emouha.

Rahotanni dake zuwa daga yankin sun ce an samu hatsarin ne ranar Alhamis a kauyen Rumuekpe dake karamar hukumar Emohua a Jihar ta Rivers, abinda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Wata majiya a yankin ta ce matasa sa sun saba fasa bututun da suka ratsa kauyukan su, suna dibar mai, kuma wannan hatsari nada nasaba da hakan.

Wani mazaunin yankin Chikwem Godwin ya shaida wa jaridar Daily Trust cewar mutane sama da 20 ake fargabar sun mutu, lura da yawan mutanen da suka yi dafifi wajen dibar man.

Wani da ya ga yadda hatsarin ya faru da ake kira Amadi ya ce daga cikin wadanda suka mutu, akwai mutane 5 da suka kone kurmus.

Kakakin rundunar Yan Sandan Jihar Rivers Nnamdi Omoni ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma kuma ya ce ba su iya tantance adadin wadanda suka mutu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *