Kar ku baiwa masu tsatsauran ra’ayi damar karbe ragamar Najeriya – Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci hukumomin tsaron kasar tare da shugabannin siyasa da su tashi tsaye wajen ganin sun murkushe duk wasu masu bukatar jefa Najeriya cikin tashin hankali ta hanyar wa’azin da suke gudanarwa.

Abubakar ya bayyana cewar mutane da dama na amfani da addini wajen mummunar fassara domin biyan bukatar kan su, saboda babu wanda ke tankwasa su, musamman daga cikin manyan addinan kasar guda biyu.

Sarkin Musulmin ya bayyana wannan matsalar a matsayin babbar kalubalen da ya addabe su, saboda haka ya dace a rungumi shirin bayar da ilimi domin kawar da matsalar tsatsauran ra’ayi a cikin al’umma.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust

Abubakar ya bukaci hukumomin Najeriya da su dauki duk matakin da ya dace wajen hana masu tsatsauran ra’ayi karbe ragamar tafiyar da kasar ta hanyar amfani da addini da kuma matakan tsaro.

Daga karshe Sarkin Musulmi ya bayyana matsalar rashin amfani da shawarwarin masana wajen shawo kan matsalolin da suka addabi Najeriya a matsayin babban kuskuren da ya sanya Najeriya a cikin yanayin da ta samu kan ta ayau.

Shugaban sojin kasa na Najeriya Lafatanar Janar Faruk Yahya ya bayyana cewar ana iya shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi kasar muddin kowa ya bada gudumawar da ake bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *