FIFA za ta kira taron tattauna yunkurin sauya fasalin gasar cin kofin Duniya

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Duniya fifa Gianni Infantino ya ce suna shirin karbar bakoncin wani babban taro na masu ruwa da tsaki cikin watan Disamba don tattaunawa kan yunkurin dawo da gasar cin kofin Duniya duk bayan shekara biyu.

A wani taron manema labarai Infantino, ya ce taron zai gudana ranar 20 ga watan na Disamba don tattara mabanbantan ra’ayoyin daidaikun mutane da kasashe game da yunkurin wanda zai basu damar tsayar da matsaya guda.

Tun a litinin din da ta gabata FIFA ta sanar da cewa za ta fara tuntubar kasashe daga ranar talata da yau alhami sai dai Infantino ya ce hukumar ta fasa wannan mataki maimakon haka za ta shirya taron na watan Disamba.

Acewarsa FIFA za ta mayar da gasar zuwa shekaru bibbiyu ne kadai idan ta samu goyon bayan kasashe kan hakan.

Tun daga shekarar 1930 ne ake gudanar da gasar ta cin kofin duniya duk bayan sheka hudu in banda lokacin yakin duniya na 2 da ya tilasta dage gasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.