Daular larabawa za ta karbi bakoncin gasar cin kofin Duniya ta Kungiyoyi

Hadaddiyar daular laraba ta samu izinin karbar bakoncin gasar cin kofin duniya ta kungiyoyi da za ta gudana a shekarar 2022.

Gasar wadda aka bunkasa ta a wannan karon za ta kunshi zakarun gasar lig-lig na nahiyoyi da zakarun gasar kalubale da kuma zakarun kasar da za ta karbi bakoncinta, ba a iya gudanar da ita bara a Japan ba saboda annobar covid-19.

Sanarwar fifa da ke tabbatar da daular ta larabawa a matsayin wadda za ta karbi bakoncin gasar ta ce za ta gudana ne a farkon shekarar 2022 sabanin yadda aka saba yinta a watan Disamba.

Wannan ne karo na biyu da ake sauyawa gasar ta cin kofin kungiyoyi lokaci inda ko a shekarar 2020 FIFA ta dage gasar daga watan na Disamban shekarar zuwa Fabarairun bana.

A bangare Turai Chelsea ce za ta wakilci nahiyar yayinda Al Ahly  ta masar za ta wakilci Afrika bangaren kudancin Afrika kuwa ko dai Palmeiras ko Flamengo na Brazil.

Bayern Munich ce tafi lashe kofunan gasar wadda sau 4 ana gudanar da ita a Daular larabawa ko da ya ke Real Madrid ta lashe gasar ta 2018.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *