‘Yan bindiga sun sace sama da mutane 830 a jihar Kaduna cikin watanni 3

Daily Trust ta ruwaito cewa, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce an yi garkuwa da mutane 830 a jihar daga watan Yuli zuwa Satumba 2021.

Ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton tsaro na kwata na 3 ga gwamnan jihar, Nasir El’rufai, ranar Laraba 20 ga watan Oktoba.

A rahoton Daily Sun, Aruwan ya kuma ce sojojin sun kashe jimillar ‘yan ta’adda 69 a lokacin da suke kai hare-hare a sassa daban-daban na jihar a cikin wannan lokaci da ya ambata.

Ya yi bayanin cewa an kashe ‘yan ta’adda da yawa yayin hare-hare ta sama kan wuraren da aka gano suna fakewa sannan an lalata sansanonin ‘yan ta’adda da yawa.

Kwamishinan ya ce daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a gundumar sanatan Kaduna ta tsakiya sun kai 732 a wurare kamar kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Igabi, Chikun da Kajuru.

Ya kuma ce an sace dabbobi 1,018 a jihar a cikin kwata na uku na shekarar tare da sace mutane 780 daga gundumar sanatan Kaduna ta tsakiya.

Aruwa ya kuma ce mutanen da suka jikkata a fadin jihar dalilin barnar ‘yan bindiga, hare-haren ta’addanci, ramuwar gayya da kuma rikice-rikicen al’ummomi sun kai 210.

Ya koka da cewa an samu rahotanni 77 da suka shafi lalata amfanin gona a fadin jihar musamman a kananan hukumomin Birnin Gwari, Igabi, Giwa, Chikun, Kachia, Kaura, Kauru da Zongon Kataf.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *