Wasu ‘Yan bindiga a Najeriya sun kashe Sarakunan Igbo biyu a Jihar Imo

Rahotanni daga jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da ba’a tantance ko su waye ba, sun kashe sarakunan gargajiya biyu a wani hari da suka kai a jihar.

‘Yan bindigar sun kai farmakin ne a yayin da ake gudanar da wani taron sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a garin Nnenasa da ke karamar hukumar Njaba, inda suka bude wuta ba kakkautawa, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar sarakunan biyu.

Sarakunan sun hada da Eze E. A. Durueburou da Eze Samson Osunwa.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Imo ta tabbatar da aukuwar lamarin ta bakin kakakinta Mike Abattam, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *