Shekaru 10 bayan kisan gillar Ghaddafi har yanzu babu zaman lafiya a Libya

Wannan Laraba 20 ga watan Oktoba ake cika shekaru 10 da juyin juya halin da ya yi sanadiyar kashe shugaban kasar Libya Muammar Ghadafi, har yanzu kasar na ci gaba da fama da tashin hankali da kuma rashin zaman lafiya.

Masu sa ido a rikicin kasar sun ce, kulla yarjejeniyar zaman lafiya ta shekara guda da kuma kudirin da bangarorin da basa ga maciji da juna a kasar suka sanyawa hannu a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya tare da shirin zaben shugaban kasar da za’ayi a watan Disamba mai zuwa, na da wahala ya warware matsalolin da suka addabi Libya.

Shugaba Ghadafi ya mulki kasar Libya na shekaru 42 bayan juyin mulkin da ya jagoranta a shekarar 1969 akan masarautar kasar, inda ya gabatar da kan sa a matsayin dan juyin juya hali, Balarabe kuma gwarzon ‘Dan Afirka, yayin da ya dinga murkushe masu adawa da shi.

A shekarar 2011 aka kifar da gwamnatin sa bayan wata zanga zangar da ta ratsar kasashen Larabawa da ta samu taimakon kungiyar tsaro ta NATO.

A ranar 20 ga watan Oktoba na shekarar ce, Yan tawaye suka cimma masa a garin san a Sirte, suka azabtar da shi da kuma hallaka shi a titin kasar, inda suka gabatar da gawar sa a kasuwa.

Mutuwar Ghadafi ta gaza samar da dimokiradiya a Libya kamar yadda masu zanga zangar wancan lokaci suka bukata, yayin da kasar ta fada cikin tashin hankali da rarrabuwar kawuna tare da samun ‘Yan tawayen dake dauke da makamai suna fada a tsakanin su, yayin da kowanne bangare ke samun goyan baya daga kasashen duniya domin mamaye man fetur din da Allah Ya wadata kasar da shi.

Tsohon shugaban kasar Libya Mouammar Kadhafi a Tripoli, 08/09/2010.

Yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a watan Oktobar bar ata bada damar kafa gwamnatin rikon kwaryar da zata jagoranci kasar zuwa zaben shugaban kasa da Yan majalisun da za’ayi a ranar 24 ga watan Disamba mai zuwa, sai dai har yanzu akwai shakku ko zaben na iya gudana cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *