Lionel Messi ya ci wa Paris St-Germain kwallaye biyu a karawar da ta doke RB Leipzig da ci 3-2 a gasar zakarun Turai ranar Talata.
Kylian Mbappe ne ya fara ci wa PSG kwallo, Sai dai Andre Silva ya farke kwallon, sannan Nordi Mukiele ya kara na biyu, inda kungiyar ta Jamus ta shiga gaba. Daga bisani Messi ya farke wa PSG, sannan ya ya kara na uku a bugun fenariti.
PSG ta sake samun wani bugun finaretin ana daf da tashi wasa, amma sai Mbappe ya barar.
Messi ya yi wasa 123 a Champions League
Kawo yanzu Messi ya ci kwallo uku a PSG a Champions League, tun bayan da ya koma kungiyar, wanda ya ci daya a wasan da suka doke Manchester City 2-0. Kuma jummular kwallaye 123 Messi ya ci a gasar Zakarun Turai, kuma 120 ya zura su ne lokacin da yake wasa a tsohuwar kungiyarsa Barcelona.