Harin bama-bamai ya kashe akalla muatane 27 a kasar Syria

Wani harin bam da ba a saba gani ba da aka kai kan wata motar sojoji a Damascus da kuma tashin bamabamai a gefen wani gari da ke hannun ‘yan tawaye a arewa maso yammacin Siriya ya kashe a kalla mutane 27 a ranar Laraba, amatsayin  hari mafi muni cikin watanni.

An tayar da bama -bamai guda biyu a kan motar sojoji a tsakiyar birnin Damascus da sanyin safiya, inda suka kashe mutane 14 a matsayin hari mafi muni da aka kai babban birnin kasar cikin shekaru hudu.

Ya zuwa yanzu babu wani bangare da ya dauki alhakin  kai harin, sai dai kuma bayan wani dan lokaci da kai harin,  sojojin gwamnatin sun yi luguden wuta tare da kashe mutane 13 a lardin Idlib, yankin da ke karkashin ikon kungiyoyin da ke daukar alhakin makamaicin wannan hari a baya.

Kamfanin dillancin labarai na kasar SANA yace “Wani harin ta’addanci da aka yi amfani da wasu bama -bamai guda biyu ya nufi wata motar bas da ke wucewa” a wata babbar gadar da ke babban birnin kasar, inda akalla mutane uku suka jikkata.

Wata majiyar soji da kamfanin dillancin labarai ya nakalto ta ce bama-baman sun tashi ne lokacin da motar ta wuce kusa da gadar Hafez al-Assad, kusa da gidan adana kayan tarihi na kasa da ke tsakiyar babban birnin Syria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *