Katafaren Kamfanin sadarwar Facebook ya amince ya biya tarar Dala miliyan 14 domin kaucewa hukuncin kotun Amurka dangane da tuhumar da ake masa na fifita baki wajen daukar ma’aikata a kasar, maimakon yan kasa.
Masu gabatar da kara a Amurka sun tuhumi Facebook da baiwa masu rike da bizar shiga kasar aiki maimakon tallata shi ga jama’ar kasa baki daya, abinda ya sabawa ka’idodin kasar.
Karar wadda aka shigar da ita a watan Disambar bara, na daga cikin jerin tuhume tuhume da ake yiwa kamfanin.
Mataimakiyar Babban Lauyan Amurka, Kristen Clarke tace Facebook bai fi karfin dokar kasar ba, saboda haka dole a ladabtar da shi.