‘Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 43 a kasuwar Goronyo da ke Sokoto

‘Yan Bindiga a Najeriya sun kai wani kazamin hari a kasuwar Goronyo da ke Jihar Sokoto inda suka kashe mutane sama da 43, yayin da suka jikkata wasu da dama.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewar maharan dauke da muggan makamai sun kutsa kai ne a kasuwar wadda ke ci mako mako inda suka bude wuta akan mai uwa da wabi.

Kakakin gwamnatin jihar Sokoto Mohammed Bello ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma  ya ce basu da cikkaken adadin mutanen da suka mutu, amma kuma yawan su na iya zarce 30.

Jami’in ya bayyana cewar harin ya auku ne lokacin da ake cin kasuwar garin, kuma tuni gwamnati ta dauki mataki akai.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Sanusi Abubakar ya ce sun tura jami’an su garin domin gudanar da bincike akan harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *