Dan wasan tsakiya na Real Madrid, Luka Modric ya caccaki yunkurin hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA wajen ganin ta mayar da gasar cin kofin Duniya duk bayan shekaru 2 sabanin 4 da aka saba.
Acewar dan wasan maimakon yunkurin FIFA na fara tuntubar manajojin kassahe kan matakin, kamata ya yi ta fara tuntubar ‘yan wasa kasancewar su abin ya fi shafa kai tsaye.
A jiya litinin ne FIFA ta sanar da cewa za ta fara wata tattaunawa da masu horar da ‘yan wasan kasashe daga yau talata don jin ra’ayoyinsu game da mayar da tsarin gudanar da gasar duk bayan shekara biyu.
Baya ga ‘yan wasan da ke caccakar yunkurin na FIFA, su kansu manyan hukumomin wasanni na Duniya da suka kunshi hukumar kwallon kafar Turai UEFA da takwararta ta kudancin Amurka CONMEBOL baya ga kwamitin shirya wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya Olympics sun yi kakkausar suka ga FIFA kan kokarin sauya fasalin gasar wadda aka saba gudanar da ita duk bayan shekaru 4 fiye da shekaru 90 da suka gabata.
Modric wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or bayan kai Croatia ga wasan karshe na cin kofin Duniya a shekarar 2018 da ya gudana a Rasha ya ce baya tunanin akwai ‘yan wasan da za su goyi bayan yunkurin na FIFA.