Liverpool ba ta shakkar haduwarta da Atletico Madrid- Klopp

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce ko kadan baya shakkar Zubin ‘yan wasan da Diego Simeone zai yi amfani da shi a wasansu na yau karkashin gasar cin kofin zakarun Turai.

Klopp wanda ya ce Simeone ya yi amfani da dabaru wajen zubin ‘yan wasanshi a bara da ya basu damar nasarar kan Liverpool da kwallaye 3 da 2 karkashin makamanciyar gasar wanda a wancan lokaci ya fitar da Liverpool bayan jumullar kwallaye 4 da 2 a gida da waje, ya ce ba kadai zubin ‘yan wasan na Simeone ne ya yi tasiri wajen hana Liverpool nasara a wasan ba, harma da matakin hana halartar ‘yan kallo da ya sanya tawagar buga wasan ba tare da cikakken karsashi ba.

Wasan na Liverpool da Atletico Madrid cikin watan Maris din 2020 shi ne wasan farko da aka fara ba tare da ‘yan kallo ba, gabanin dakatar da wasannin dungurugum na tsawon watanni saboda coronavirus.

Manajan na Liverpool wanda ke amsa tambaya gaban manema labarai gabanin wasan na yau, ya ce tawagar tasa na shirin tunkarar kungiya mafi karfi yanzu a Spain amma dukkaninsu suna da nasu banbance-bambancen.

Leave a Reply

Your email address will not be published.