Firaministan Spain Pedro Sanchez ya sha alwashin haramta aikin karuwanci a kasar, wanda ya bayyana shi a matsayin bautar da mata.
Yayin da yake tsokaci a wajen rufe taron jam’iyyar sa na kwanaki 3 da akayi a Valencia, Sanchez ya bayyana manufofin da gwamnatin sa ta gabatar wadanda yace sun taimaka wajen shawo kan rikice-rikicen da ake samu da kuma batun karin albashi.
Firaministan ya yiwa mahalarta taron alkawarin cewar zai aiwatar da shirin haramta karuwancin a fadin kasar saboda abinda ya kira yadda mummunar dabi’ar ke zama kamar bautar da mata.