Matashin Bakano, matukin jirgin sama da ya koma sana’ar dinki

Ishaq Ibrahim Abubakar matashi ne mai shekaru 38 a duniya kuma ya na daga cikin matasa 100 da gwamnatin Kano ta dauka nauyin horarwarsu domin zama matukan jirgin sama a kasar ketare a 2013.

Sai dai, duk da kammala horarwar cike da nasara kuma ya dawo gida, dole ta sa ya koma sana’ar dinki domin rufawa kai asiri.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an haifa Abubakar a kwatas din Fagge da ke karamar hukumar Fagge ta jihar Kano. Ya yi dukkan karatunsa a jihar har zuwa matakin digirin farko a jami’ar Bayero da ke Kano.

Cike da hazaka Abubakar ya samu lasisin tukin jirgin ‘yan kasuwa da daraja ta farko bayan kammala karatunsa a Jordan.

Amma kuma tun bayan dawowarsa Najeriya a 2015, bai samu damar tuka jirgi ba. Ya cigaba da zama babu aikin yi duk da ya na da shaidar karatuttuka a Multi-Crew Course (MCC) certificate da Crew Resource Management Certificate (CRM) da jarabawar RELTER.

Wannan halin da Abubakar ya shiga ya na da alaka ne da wasu bukatu wadanda suka shafi makuden kudi da za a kashe kafin a dauke shi aikin fara tukin jirgin sama.

Abubakar ya ce:

“Bukata ce a kowanne sashi na duniya cewa bayan an kammala karatun tukin jirgi, akwai wata horarwa da za a yi domin kwarewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.