Masu adawa da gwamnatin Soji sun ci gaba da zanga-zanga a Sudan

Dubban masu adawa da gwamnatin mulkin Soji a Sudan sun ci gaba da zanga-zangar kin jinin Firaminista Abdallah Hamdok a sassan kasar, zanga-zangar da shugaban ya bayyana da mafi munin rikici a karkashin mulkinsa.

Masu zanga-zangar sun yi dafifi a tsakar birnin Khartoum gab da fadar shugaban kasa don nuna kyamarsu da gwamnatin rikon kwaryar sojojin wadda suka kira mai kama karya da ta kassara tattalin arziki tare da lalata tsarin siyasar kasar.

Guda cikin jagororin masu zanga-zangar Ali Askouri ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa a jiya lahadi cewa za su ci gaba da zaman dirshan a wajen fadar shugaban har zuwa lokacin da bukatarsu za ta biya.

Tun daga asabar din karshen makon da ya gabata ne dubunnan al’ummar ta Sudan suka faro zanga-zangar amma ta zaman dirshan a tsakar birnin na Khartoum gab da fadar gwamnatin kasar don kalubalantar salon kamun ludayin Firaminista Abdallah Hamdok ta fuskar tattalin arziki da siyasa.

Masu zaman na dirshan na bukatar rushe gwamnatin rikon kwaryar ta Sudan tare da neman majalisar kolin kasar da bangaren fararen hular da ke cikin tafiyar gwamnati su jiya baya ga bangaren Sojin.

Zanga-zangar zaman dirshan din na zuwa a wani yanayi da aka samu rarrabuwar kai tsakanin mukarraban gwamnatin rikon kwaryar kasar dai dai lokacin da wani bangare ke goyon bayan gwamnatin mai ci a bangare guda kuma dayan sashen ke biyayya ga tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *