Real Madrid da Gwamnatin Jihar Ribas dake Najeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin kai don inganta wasanni tsakanin yara da matasa a Kwalejin Real Madrid a Fatakwal.
A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kelvin Ebiri, Mataimaki na Musamman kan harkokin Yada Labarai ga Gwamnan Jihar Ribas, sanya hannun ya gudana ne a karshen mako a dakin taro na Real Madrid Sport City, dake Madrid na Spain.

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, a madadin Gwamnatin Jihar Ribas da Mista Enrique Sanchez, Mataimakin Shugaban zartarwa, Gidauniyar Real Madrid da Mista Jihad Saade, Shugaba, Interact Sports, ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar.