Barcelona ta yi nasarar doke Valencia da ci 3-1 a wasan da suka fafata a gasar La Liga a Camp Nou ranar Lahadi.
Ansu Fati ne ya farke wa Barcelona kwallon da aka fara zura mata, kuma na farko da matashin dan wasan ya ci a La Liga tun bayan kusan shekara daya da ya yi jinya.
Valancia ta fara jefa kwallo minti biyar da fara wasa ta hannun Jose Gaya, amma Fati ya farke, kafin kuma Barcelona ta ci na biyu ta hannun Memphis Depay a bugun fenariti, sannan Philippe Coutinho wanda ya shiga karawar daga baya ya kara na uku, kuma na farko tun bayan wata 11.
Da wannan sakamakon Barcelona ta koma ta bakwai a teburin La Liga da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid ta biyu da tazarar maki biyar tsakaninta da Real Sociedad wadda ke jan ragama teburi.