An gudanar da zaben shugabancin PDP lafiya a Adamawa da Kwara.

Babbar Jam’iyyar Adawa a Najeriya ta PDP ta gudanar da tarukan zaben shugabanninta a wasu jihohin kasar da suka hada da Adamawa da Oyo da Kwara a karshen mako. Sai dai zaben ya bar baya da kura, ganin yadda rikici ya barke a tsakanin mambobinta.

Koda dai an gudanar da taron cikin lumana a Adamawa da Kwara, amma ba a wanye lafiya a jihar Oyo ba, inda ‘yan jagaliya suka  kaddamar da hari kan wani jigo a jam’iyyar ta PDP mai suna Omolaja Alao.

Mista Alao mai shekaru 70 da doriya, shi ne shugaban Karamar Hukumar Arewa Maso Gabashin Ibadan, yayin da ‘yan dabar siyasar suka kai masa hari a daidai kofar shiga filin taron.

A jihar Lagos ma, rahotanni sun tabbatar cewa, an soke gudanar da irin wannan taro sakamakon tashin hankalin da ya barke a wurin taron na dandalin Tafawa Balewa da ke tsibirnin birnin Lagos.

Ana gab da fara zaben ne dai, wani gungu na ‘yan dabar siyasar ya  yi dirar mikiya kan jama’a tare da tarwatsa taron, lamarin da ya sa ala tilas aka jingine zaben.

Kodayake jam’iyyar ta PDP a Lagos ta bakin Sakatarenta mai barin gado, Taofik Gani, ta zagi APC da shirya mata manakisa ta hanyar turo wadannan matasa da suka wargaza mata sha’ani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *