WHO ta sanar da karuwar masu tarin fuka karon farko cikin shekaru 10

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi ikirarin samun karuwar wadanda ke kamuwa da cutar tarin fuka ko kuma TB da adadi mai yawa irinsa na farko cikin fiye da shekaru 10 da suka gabata, wanda ke da nasaba da tasirin cutar covid-19.

Hukumar WHO cikin wata sanarwarta yau Alhamis ta ce karuwar masu kamuwa da cutar ta TB ko kuma tarin fuka na da nasaba da yadda annobar covid-19 ta hana aikin yaki da cutar duk da irin hadari da kuma saurin yaduwarta.

WHO ta ce yanzu haka akwai alkaluman mutum miliyan 4 da dubu 1 da kef ama da tarin na fuka ko kuma TB a sassan Duniya, wanda ya kusan ninka adadin da ake da shi a shekarar 2019 na mutum miliyan 2 da dubu 900.

Hukumar ta ce alakanta rashin daukar matakan da suka dace a yaki da cutar matsayin dalilin da ya ta’azzara yawan masu fama da ita, musamman bayan bullar cutar corona da ta tilasta dakatar da yaki da sauran cutuka masu hadari ciki har da tarin na TB.

Sanarwar ta ruwaito shugaban hukuma Tedros Adhanom Gebreyesus na cewa karuwar masu fama da tarin na fuka a sassan Duniya, ya nuna bukatar da ake da ita wajen zage damtse a yaki da cutar mai saurin yaduwa, ta hanyar wadata asibitoci da cibiyoyin lafiya da magungunanta baya ga rigakafin dakile yaduwarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *