Paraguay ta kori kocinta bayan shan kashi a hannun Bolivia

Paraguay ta kori kocin ta Eduardo Berizzo dan kasar Argentina bayan da Bolivia ta lallasa su da ci 4-0 a wasan neman gurbi a gasar cin kofin duniya.

Nasarar da aka yi a kan Paraguay a wasansu na jiya Alhamis ta bar kasar amatsayin ta takwas a wasannin na sharen fagen shiga gasar neman cin kofin duniya da Qatar zata karbi bakwanci a badi, inda ake daukar kashe hudu a kowane yanki.

Hukumar kwallon kafar Paraguay ta ce” cikin kwanaki masu zuwa za ta sanar da sabon mai horar da tawagar kasar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *