Inter ta shiga sahun kungiyoyin da ke neman dauko dan Najeriya Onuachu

Inter Milan ta shiga sahun kungiyoyin kwallon kafa dake neman dauko dan wasan gaba na Najeriya Paul Onuachu a kasuwar musayar ‘yan wasa dake tafe.

Onuachu ya sanya hannu kan tsawaita kwantiraginsa da kulob dinsa na Belgium, KRC Genk, amma ya dauki hankalin manyan kulob – kulob na Turai, ciki har da zakarun Spain, Atletico Madrid.

Jaridar Italiya Football tace, Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta shirya tsaf don ganin ta sayo dan wasan gaba don cike gibin kai hare-hare bayan tafiyar Romelu Lukaku zuwa Chelsea.

Kafin ya koma Genk a shekarar 2019, Onuachu ya buga wasanni 181 a FC Midtjylland inda ya ci kwallaye 74.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *