Hukumomin Kamaru sun bukaci kwantar da hankula a yankin ‘yan aware

Hukumomi a yammacin Kamaru da ake amfani da turancin Ingilishi sun bukaci a kwantar da hankula bayan da wani Jardama ya kashe wata yarinya ‘yar makaranta kafin daga bisani fusatattun mutane suka farmasa a yankin da ke fama da tashin hankali tsakanin mayakan ‘yan aware da sojoji.

Lamarin ya faru ne a birnin Buea, hedikwatar yankin Kudu maso yammacin Kamaru da ake amfani da turancin Ingilishi, inda ‘yan aware dake neman ballewa domin kafa jamhuriyar Ambazonia ke fafatawa da sojojin gwamnatin kasar da ke da rinjayen Faransanci.

Gwamnan yankin Bernard Okalia Bilai dake kiran al’umma ta kafar radiyo da talabijin din kasar CRTV, yace lamarin abin bakin ciki ne da kuma takaici,”.

Da yake shaidawa manema labarai, Blaise Chamango, shugaban wata kungiyar kare hakkin bil’adama a yaki, yace  lamarin ya faru ne, bayan da wani jandarma ya bude wuta kan wani mota da wata mata ke kai ‘ya’yan ta makaranta a wani shingen bincike, inda karamar yarinyar ta mutu sakamakon raunin bindiga da ta samu.

Matakin da ya fusata mutane tare da mayar da martani nan take ta hanyar afkawa jami’in jandarma, inda  Sama da mutane 500 suka fito suka yi tattaki da gawar (yarinyar) zuwa ofishin gwamna.

Leave a Reply

Your email address will not be published.