Taliban ta tabbatar da harin kunar bakin wake yayin sallar juma’a yau a wani masallacin mabiya shi’a da ke birnin Kandahar a Afghanistan wanda ya hallaka mutane 41 tare da jikkata wasu 74.
Harin ya zo mako guda bayan makamancinsa a arewacin birnin Kunduz wanda kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa.
Har kawo yanzu dai babu kungiyar da ta sanar da daukar nauyin kaddamar da harin, said ai IS wanda ke matsayin babbar barazana ga Taliban na ci gaba da kaddamar da makamantan hare-haren tun bayan da kungiyar ta kwace iko da Afghanistan a farkon watan Agusta.
Wani jami’in Taliban da ke kula da tsaron yankin, wanda bai bayyana sunansa ba, ya ce bincikensu ya gano cewa, maharin ya tashi bom din da ke jikinsa ne a cikin masallacin lokacin da ake tsaka da sallah.
Da farko babban jami’in lafiyar da ke kula asibitin Mirwais ya shaidawa AFP cewa sun samu gawarwakin mutum 33 baya ga wasu 74 da suka samu raunuka a harin.