Za mu yi duk mai yiwuwa don rike Mbappe a PSG – Pochettino

Mauricio Pochettino ya dage cewa PSG za ta yi ‘duk abin da za ta iya’ don ganin ta ci gaba da rike Kylian Mbappe, yana mai cewa dole ne kungiyar dake taka leda a Faransa ta ‘sauyawa dan wasan ra’ayi, yayin da kwantiragin dan wasan zai kare a bazara mai zuwa, dai-dai lokacin da Real Madrid ke zawarcinsa.

Yarjejeniyar dan wasan mai shekaru 22 a Parc des Princes za ta kare a bazara mai zuwa kuma zai sami ‘yancin tattaunawa da kungiyoyin kasashen waje daga watan Janairu, tare da tafiya a kyauta a shekarar 2022.

Mbappe ya nanata matakinsa na barin kungiyar Paris Saint Germain a sabuwar kakar wasanni mai zuwa – kuma burinsa shine komawa doka leda a gasar Lalkigar Spain tare da Real Madrid.

To saidai Pochettino ya dage cewa kungiyar ta Ligue 1 za ta yi iya bakin kokarinta don ci gaba da zama da Mbappe a Paris.

Duk da yace dan wasan na da zabi, amma baza suyi kasa a guiwa ba, saboda da batu ne da ya shafi wanda suke kallo a matsayin daya daga cikin fitattun’ yan wasa duniya a shekaru 22.

A bangare daya, Pochettino ya kuma yi Karin haske dangane da lafiyar Sergio Ramos, wanda har yanzu bai buga wa kulob din wasa ba tun bayan komawarsa a wannan kakar wasanni.

Pochettino ya kara da cewa ” Abin takaici, Ramos bai fara horo da kungiyar ba tukuna, amma yana kusa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *