An tsinci gawar wata tsohowa mai shekaru 77 da aka fillewa kai a gidanta

Hukumomin Faransa sun gano gawar wata mata mai shekaru 77 da aka fillewa kai a gidanta da ke wani wurin shakatawa da ke kudancin kasar.

Wata majiyar ‘yan sanda, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa a halin yanzu hukumomi ba sa kallon lamarin da ta’addanci saboda ba musu gabatar da karar kan ayyukan ta’addanci bane ke bincike.

Majiyar ‘yan sandan tace an gano gawar matar a gidanta dake Agde da ke yankin Herault a gabar tekun Mediterranea a kudancin Faransa.

‘Yan sanda sun ziyarci gidan tsohuwar ce bayan da danta ya sanar da su rashin jin duriyarta, sakamakon yadda suka saba waya kullum, sannan kuma ya leka gidan ta hoton bidiyo kuma ya kalli wani abu kamar inuwa a ƙasa.

Wata majiyar kuma tace, kan matar na kan tebur kusa da gawar, kuma babu wani alamun balle kofar shiga dakin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *