Turai ta saka biliyan daya a gidauyniyar tallafa wa Afghanistan

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce ta sanya Yuro biliyan 1 cikin gidauniyar da aka kafa don tara kudaden da za’a tallafa wa jama’ar Afghanistan.

Dama tun bayan da Taliban suka kifar da gwamnatin Ashraf Ghani tare da karbe iko da gwamnatin Afganistan ne hukumomi a duniya suka bayyana bukatar da ke akwai na samar da wata gidauniya da za a tallafa wa jama’ar Afghanistan.

Komawar Afghanistan hannun Taliban dai ya janyo matsananci matsalar tattalin arziki da talauci da yunwa tsakanin jama’ar kasar, inda ta kai har mutane na sayar da kayan amfanin su na gida don sayen abinci.

Da ta ke jawabi shugaban kungiyar Ursula Von der Leyen ta ce Tarayyar Turai ta sanya wadannan zunzurutun kudi cikin gudauniyar ne don tallafa wa jama’a kasar da ke fuskantar barazanar yunwa da bakin talauci ba don wata manufa tata ta kashin kai ba.

Manyan kasashe da ke da karfin tattalin arziki na G20 ne dai suka amince da tattara kudin a yayin taron su, inda suka tabbatar da cewa za’a hada Yuro miliyan 250 kari kan yuro miliyan 300 da tun da fari tarayyar Turan ta ayyana bukatar tarawa don ceto jama’ar Afghanistan daga tagayyara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *