MDD ta zargi Najeriya da kin baiwa mata mukaman shugabanci

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar, Najeriya ce kasar da tafi kin baiwa mata mukaman shugabanci a matakin zabe ko kuma nadi.

Jami’ar kula da harkokin mata ta Majalisar Angela Muruli ta bayyana haka, inda ta bukaci sake fasalin shugabancin kasar wajen baiwa mata akalla kashi 50 na mukaman zaben da za’ayi a kasar na shekarar 2023.

Muruli tace yana da muhimmancin matan Najeriya su shiga a dama da su a siyasa, saboda shigar su zai bada damar daukar matakan inganta rayuwar al’umma.

Jami’ar tace da farko dai Najeriya ce ke da wakilai mata mafi karanci a Yankin Afirka dake kudu da sahara da kuma duniya, saboda haka abin takaici ne ga kasar da tafi kowacce a Afirka na rashin baiwa rabin al’ummar ta wakilcin da ya dace.

Muruli tace a zamanin da ake tafiya yanzu da mata suka fi maza yawa, yana da muhimmanci a dinga raba dai dai na mukamai, inda akalla kowanne jinsi zai samu kashi 50.

Leave a Reply

Your email address will not be published.