Ga alama Mali ba za ta iya gudanar da zabe a badi ba

Ministan Harkokin Wajen Mali Abdoulaye Diop, ya ce abu ne mai wuya kasar ta iya gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a ranar 27 ga watan ?Fabairu mai zuwa kamar dai yadda aka tsara.

Minista Diop, wanda ke ganawa da takwaransa na kasar Marocco Nasser Bourrita, ya ce gudanar da zabubukan a wannan rana zai dogara ne da yanayin tsaro a kasar ta Mali. 

Cewa dole ne a gudanar da zabe ranar 27 ga watan Fabarairu, a ganina bai kamata kasashe aminai na yi mana irin wannan barazana ba, abin da ya kamata shi ne su duba yanayin da kasar nan ke ciki tare da taimaka wa Mali don fita daga cikin matsalolin da take fuskanta. inji Diop.

Sai dai a karin bayanin da ya yi, Ministan ya ce, ba wai hakan na nufin cewa Mali ba ta da niyyar shirya zabubuka ba ne, tabbas shugaba Goita na cikin shiri don mika mulki a hannun zababbiyar gwamnati, amma za a yi hakan ne tare da amincewar al’ummar kasar Mali a cewarsa.

‘Yan kasar Mali da dama ne ke ganin cewa tamkar, ana ba su umurni ne daga ketare, musamman zargin cewa kasashen da muke da amintaka da su ne ke shata mana yadda za mu tafiyar da kasarmu, wannan ba zai taba yiyuwa ba. Inji Ministan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *