Wani mutum ya datse ‘yar yatsar jami’in ɗan sanda da cizo a Legas

An gurfanar da wani mutum mai shekaru 29, Samuel Jacob, a gaban alkalin kotun Majistare da ke Badagry a Legas, a ranar Talata, kan tuhumarsa da cije ‘dan yatsar dan sanda, Saja Musa Hassan.

‘Yan sandan na tuhumar Jacob, wanda ba a bayyana adireshinsa ba da laifin duka da yin rauni kamar yadda ta zo a ruwaiyar The Punch.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Clement Okuiomose ya shaidawa kotu cewa wanda aka yi kararsa ya aikata laifin ne a ranar 3 ga watan Oktoba misalin karfe 11.30 na safe a Oloko, Badagry a Legas.

Okuiomose, ya kuma ce wanda ake kararsa antayawa Saja Hassan fetur a yayin da ya ke gudanar da aikinsa da doka ta halasta masa, ruwayar The Punch.

Laifin, a cewa da sanda mai shigar da karar ta saba wa sashi na 246 da 174 da dokar masu laifi na jihar Legas na shekarar 2015.

Amma wanda aka gurfanar ya musanta aikata laifukan da ake zarginsa.

Alkalin kotun, Mr Fadaunsi Adefioye, ya bada belin wanda ake zargin a kan kudi Naira Dubu Dari Biyu (N200,000) da kuma mutane biyu wadanda za su tsaya masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *