Tattaunawa ta ci gaba tsakanin Iran da Saudiya don gyatta alakarsu

Kasashen Saudi Arabia da Iran da basa ga maciji da juna, sun bayyana samun ci gaba a tattaunawar da suke domin dinke barakar dake tsakanin su, duk da ikrarin masana cewar har yanzu akwai sauran tafiya.

Kasashen biyu da ke matsayin manyan makiyan juna kuma jagororin akidu biyu da basa ga maciji wato Sunnah da Shi’a yanzu haka na kokarin dinke barakar da ke tsakaninsu ne don tafiya tare ko da ya ke bayanai na cewa abu ne mai wuya ayi gaggauwar cimma jituwar saboda batutuwa da dama da bangarorin biyu suka yi hannun riga akai.

Alaka ta kara tsami tsakanin bangarorin biyu ne tun bayan harin da masu zanga-zanga suka kai Ofishin jakadancin Saudi Arabiya da ke Tehran wanda ke zuwa bayan zargin kasar da kisan wani babban malamin Shi’a.

A baya-bayan nan ne aka fara tattaunawar farfado da dangantakar tsakanin kasashen na Iran da Saudiyya inda aka ga wasu jagorori daga kasashen biyu na tattaunawa da juna wanda ba’a saba gani duk da banbancin ra’ayin kasashen biyu a al’amuran da suka shafi rikicin gabas ta tsakiya musamman yakin kasar Yemen wanda Iran ke goyon bayan ‘yan Tawaye Saudiyya kuma ke mara baya ga gwamnatin kasar.

Tun farko tsohon shugaban Iran Hassan Rouhani ya amince da tattaunawar bangarorin biyu gabanin samun ci gaba daga sabon shugaba Ibrahim Raisi wanda ya sake bude kofar gyatta alakar.

Kamar yadda fadar shugaban Iran ke tabbatarwa da yiwuwar nan gaba kadan kasashen biyu su sake bude Ofisoshin jakadancin juna don ci gaba da hulda.

Shi ma Ministan harkokin wajen Saudiya Yarima Faisal bin Farhan ya bada tabbacin zaman fahintar juna a tsakanin kasashen 2 wanda ke nuna da yiwuwar kwalliya ta biya kudin sabulu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *