Hukumar kwastam ta ƙasa (NCS) reshen jihar Katsina ta bayyana cewa yan fasa ƙwaurin shinkafa na yin zagon ƙasa a yaƙin da ake da yan bindiga a Katsina.
Wada Chedi, muƙaddashin kwanturolan kwastan na jihar, shine ya bayyana haka a wata fira da manema labarai a ofishinsa ranar Litinin da yamma.
Premium times ta ruwaito shi yana cewa yan sumoga na taimakawa yan ta’addan wajen tsallake matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka.
Mista Chedi ya bayyana cewa masu aikin sumoga sun nemo sabbin hanyoyin kaiwa yan bindiga kayayyakin abinci da sauransu.
Yace yan fasa gwaurin na amfani da manyan tankuna domin ɗaukar man fetur su kaiwa yan ta’addan a cikin jeji.
Yace:
“Kwanan nan, mun kama motocin Peugeot 504, waɗanda yan sumogan suka kirkiri sabbin tankunan man fetur kuma suka cikasu taf da mai.”
“Yan fasa kwaurin suna zuwa gidajen man fetur sun cika waɗannan tankunan, sannan su siyarwa yan bindiga.”